Tambata ta 6. Menene Ladubban Maƙoci?

Amsa: 1. Ina kyautata wa maƙoci ta hanyar magana da aiki, kuma ina taimaka masa idan ya buƙaci taimako na.

2. Ina mishi barka idan yana farin ciki da idi (sallah ƙarama ko babba) ko aure ko ma wanin haka.

3. Ina gaida shi idan ya yi rashin lafiya, kuma ina taya shi alhini idan wata masifa ta afka ma sa.

4. Ina ba shi irin abin cin da nayi gwargwadon iko.

5. Ba na riskar da cuta da shi, da wata magana ko da wani aiki.

6. Ba na damun sa ta ɗaga murya, ko in yi mishi leƙen asiri, kuma ina yin haƙuri da shi.